1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dokokin Girka ta bada haɗin kai ga Firaminista

November 5, 2011

Bayan rinjayen da ya samu a Majalisa, Firaministan Girka George Papandreou ya gana da shugaban ƙasa domin gabatar masa da shawara girka gwamnatin haɗin kan ƙasa.

https://p.dw.com/p/135cA
Hoto: picture alliance/dpa

Majalisar Dokokin ƙasar Girka ta kaɗa ƙuri´ar amincewa da fasalin ceton ƙasar da Ƙungiyar Tarayya Turai ta ƙaddamar.Ba zato ba tsammani ,Firaministan Girka ya samu nasara shawo kan 'yan majalisar saɓanin hasashen manazarta.

Daga jimlar 'yan majalisa 300,153 suka bada haɗin kai ga Firaministan a yayin da 145 suka kin amincewa.

A cikin jawabin da yayi gaban 'yan Majalisar, Papandreou ya yi watsi da bukatar jam´iyun adawa ta shirya zaɓe, saidai yayi alƙawarin haɗuwa da shugaban ƙasar Girka domin bayyana masa shawara rusa gwamnati mai ci yanzu, domin maye gurbinta da gwamnatin wucin gadi ta haɗin kan ƙasa.

Jim kaɗan kamin kaɗa ƙuri´ar, shugaban hukumar zartaswa na Ƙungiyar Tarayya Turai Jose Manuel Barrosso yayi hannunka mai sanda ga ƙasar Girka tare da cewa:

"Idan ƙasa ta kasance memba a cikin Ƙungiyar ƙasashen Euro, ko dama ma cikin wace irin ƙungiya ce yauni ya rataya kan ta ta bi dokokin wannan ƙungiya.To amma mutanen Girka suke yuka da nama, suna da yancin yanke hukunci da zabin su."

Wannan rikici na kasar Girka shine ma ya mamaye taron shugabanin ƙasashen G20 da aka kamalla jiya a birnin Cannes na kasar Faransa.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman