Majalisar dokokin Iran ta zabi sabon shugaba
May 28, 2012Sabuwar majalisar dokokin Iran ta zabi babban abokin hammayar siyasan cikin gida na shugaba Mahmud Ahmedinejad a matsayin shugabanta. Ali Laridjani ya sami kuri'u 173 a yayinda mai kalubalantarsa Gholam Ali Hadad Adel ya samu kuri'u 100.
Mai shekaru 55 na haihuwan ya jagoranci hadin kan jamiyyu masu ra'ayin rikau wadanda suka yi nasara a zaben 'yan majalisar dokokin, bayan da jamiyyar masu neman sauyi ta kauracewa zaben. Haka nan kuma, ana masa kallon mai mafi yawan magoya baya a zaben shugaban kasar da za'a gudanar a badi idan Allah ya kai mu, inda ake sa ran shugaba Ahmedinejad ba zai iya tsayawa takara ba. Akidar Lardjani ya zo daidai da na shugaban addinin kasar wato Ayotullah Ali Khanemi.
Amma duk da cewa siyasarsa na ketare da kuma rikicin makamashin nukiliyar kasar, iri daya ne da na Ahmedinejad, ana masa kallon mai matsakaicin ra'ayin wanda bisa dukkan alamu zai iya cimma wata matsaya mai a'ala dangane da batun makamashin.
Mawallafiya: Pinado Abdu waba
Edita: Usman Shehu Usman