Isra'ila na shirin haramta wa MDD aikin agaji a Falasdinu
October 28, 2024Majalisar dokokin Isra'ila na shirin kada kuri'a a Litinin din nan kan wasu kudurori biyu masu sarkakiya, da za su haramta wa hukumar kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA aiki a yankin baki-daya.
Dukkan 'yan majalisar na bangaren gwamnati da na adawa sun amince da ayyana UNRWA a matsayin ta ta'addanci, lamarin da zai haramta wa Isra'ila mu'amala da ita baki-daya, tare da dakatar da ita daga yin aiki a duk inda Isra'ila ke da iko.
Karin bayani:MDD ta yi watsi da yunkurin soke hukumar agajin Falasdinu
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kakkausan suka kan wannan kudurin doka, wanda ya bayyana a matsayin yunkurin sanya tarnaki kan shirin agaza wa mabukata da ke cikin halin tagayyara a wannan yanki na zirin Gaza da yammacin kogin Jordan, har ma da gabashin birnin Kudus.
Isra'ila ta jima tana zargin hukumar ta UNRWA da alaka da kungiyar Hamas ta Falasdinawa.
Iran ta gargadi Isra'ila da cewa ta jira mummuna martanin da zai biyo bayan harin ramuwar gayyar da ta kai mata birnin Tehran ranar Asabar.
Karin bayani:Spain ta ware kudade ga ayyukan jin kai a Gaza
Tuni dai ministan harkokin wajen Burtaniya David Lammy ya yi kira ga bangarorin biyu da su kauce wa haddasa rincabewar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
Mr Lammy ya tattauna da takwarorinsa na kasashen biyu ta wayar tarho, inda ya ja hankalinsu da su hakura da ci gaba da takalar juna.