Dokokin Corona sun shiga dokar Jamus
November 18, 2020Majalisar dokokin Jamus ta amince da gyara dokokin kasar da zai ba wa gwamnati ikon tilasta wa al'umma bin dokokin yaki da annobar Corona. Kudurin da gwamnatin Merkel ta gabatar gaban majalisar, ya samu rinjaye da kuri'u 415, yayin da 'yan majalisu 236 suka ki nuna goyon baya, takwas kuma suka yi rowar kuri'unsu.
Jam'iyyun hamayya sun koka kan yadda dokar za ta takure hakkin 'yan kasa, amma ministan lafiya Jens Spahn ya kare kudurin da cewa "Ba za a tilasta mutane yin rigakafin cutar ba."
Majalisar zartaswar kasar Bundesrat za ta duba batun tare da fatan Shuagaban kasa Frank-Walter Steinmeier zai rattaba wa kudurin hannu ya zama a doka. Nasarar amincewa da kudirin a majalisa, ya zo a dai-dai loakcin da 'yan sanda suka kama daruruwan masu zanga-zangar adawa da matakan gwamnati na yaki da cutar Corona.