Majalisar dokokin Ukraine ta zaɓi firaminista
December 13, 2012Talla
Mykola Azarov wani na hannu daman shugaba Viktor Lanoukovitch ne dai, kuma an gudanar da zaɓen cikin wani yanayi na tashin hankali da aka soma tun jiya na bai wa hamata iska,tsakanin yan' majalisun na majoriti da kuma na addawa waɗanda suka ce a kwai kura kurai a cikin tsarin zaɓen.
'Yan majalisun 252 suka kaɗa ƙuri'a amincewa da takarar' tasa yayin da 226 suka kaɗa ƙuri'a ƙin ammincewa. jam'iyyun siyasar addawa waɗanda suka haɗa da na tshohuwar firaministan Jouliya Timochenko; da ta ɗan danben boxe ɗin nan Vitali Klitsko dukanin su suna addawa da zaɓen.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Awal