1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar EU ta goyi bayan amincewa da kasar Falasdinu

Mohammad Nasiru AwalDecember 17, 2014

Majalisar da ke birnin Strasbourg ta ce amincewa da kasar Falasdinu batu ne na daidaikun kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU.

https://p.dw.com/p/1E6My
Paris Protest von Palästinensern ARCHIV 2009
Hoto: picture-alliance/dpa

Bayan mahawara ta tsawon lokaci majalisar dokokin Turai ta nuna goyon baya ga amincewa da kasar Falasdinawa. Sai dai majalisar da ke birnin Strasbourg ta ce dole wannan matakin ya tafi kafada da kafada da sake komawa teburin tattauna batun zaman lafiya. Wakilan majalisar suka ce wanzuwar kasar Isra'ila da ta Falasdinu ita ce hanya daya tilo ta warware rikicin.

Bisa matsin lambar masu ra'ayin mazan jiya, an yi watsi da bukatar da masu ra'ayin sauyi da masu rajin kare muhalli suka gabatar da ke kira ga dukkan kasashe 28 na kungiyar EU da ba da wata-wata ba, su amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cikakken 'yancin kai. Yanzu majalisar ta ce amincewa da kasar Falasdinu batu ne na daidaikun kasashen kungiyar EU.

Duk da kashedi daga Amirka, a wannan Larabar mahukuntan Falasdinu za su gabatar da wani kuduri gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na neman Isra'ila ta kawo karshen mamayen da take wa yankunansu.