1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Girka ta amince da bukatun Alexis Tsipras

Papadimitriou/AwalAugust 14, 2015

Da kyar da gumin goshi Firaministan Girka Alexis Tsipras ya sake tsallake rijiya da baya. Godiya ta tabbata ga 'yan adawa, sabon shirin tallafi da Firaministan ya gabatar ya samu amincewar majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/1GFks
Griechenland Beratung Hilfspaket Parlament
Hoto: Reuters/C. Hartmann

((Da kyar da gumin goshi Firaministan Girka Alexis Tsipras ya sake tsallake rijiya da baya. Godiya ta tabbata ga 'yan adawa, sabon shirin tallafi da Firaministan ya gabatar ya samu amincewar majalisar dokoki. Sai dai bisa ga dukkan alamu ba za a kaucewa sabon zabe ba, inji Yannis Papadimitiou a cikin wannan sharhi da ya rubuta. Mohammad Nasiru Awal na dauke da karin bayani.))

Tun ba yau ba yake tabbas cewa Firaministan Girka Alexis Tsipras ya rasa rinjaye a kan manufarsa. A cikin watannin da suka wuce Firaministan mai ra'ayin sauyi ya sha dogaro kan 'yan adawa masu ra'ayin mazan jiya ko 'yan social democrat a majalisar dokoki don ceto kawancensa na 'yan ra'ayin sauyi da ke fama da baraka. A kwanakin bayan nan ma majiyoyin gwamnati sun nuna cewa Firaministan ka iya rasa goyon baya gaba daya a majalisa idan 'ya'yan jam'iyyarsa da za su jefa kuri'ar amincewa da sabon shirinsa na tallafi ba su kai wakilai 120 ba.

Yanzu dai an kai gaci. Bayan zaman mahawara na tsawon lokaci da wakilai 300 na majalisar suka yi, wakilai 117 na jam'iyyarsa ta Syrisa suka kada kuri'ar amincewa da sabon shirin, 32 suka nuna adawa sauran kuma suka yi rowar kuri'unsu. Firaministan ya sake samun nasara amma da gagarumin taimako daga bangaren 'yan adawa. Sai dai 'yan adawa sun yi mamaki yadda aka yi ta cece-kuce tsakanin daidaikun wakilan gwamnati, abin da ya ta kawo jinkiri a zaman majalisar. Hakan ma ya sa kakakin jam'iyyar 'yan ra'ayin mazan jiya yin korafin cewa zauren majalisar ba kwamitin tsakiya na 'yan ra'ayin sauyi ba, in da za a warware matsalarsu ta cikin gida. Ya ce wannan kan bai dace ba. Ba kuma za a ci gaba da haka ba.

Ya ce ba zai yiwu ba Firaministan kashi 50 cikin 100 na 'ya'yan jam'iyyarsa su goyi bayan shirinsa na tsimi, amma sauran kashi 50 cikin 100 su kafa wani kwamitin gwagwarmaya da ke adawa da abin da suka kira 'yan mulkin mallaka na kungiyar EU.

Bugu da kari an lokacin mahawarar shugaban 'yan adawa karara ya nuna cewa daga ranar Litinin za a yi bankwana da goyon baya da suka aka ba wa jam'iyyar sauyi.

Saboda haka Tsipras bai da zabi face ya fara shirye-shiryen kiran sabonn zabe. Sai dai hakan ba zai yiwu nan-take ba sain watakila karshen wata lokacin da za a yi maganar kuri'ar gwajin farin jinin Firaministan. Wannan wata dabara ce ta shafa wa bijirarrun 'ya'yan jam'iyyarsa kashin kaji dangane da rugujewar gwamnatin 'yan ra'ayin sauyi ta farko cikin tarihin kasar ta Girka.

Griechenland Ministerpräsident Alexis Tsipras im Parlament die Zeit läuft aus
Firaminista Alexis TsiprasHoto: Reuters/C. Hartmann

Su ma 'yan adawa ba za su yi farin cikin gudanar da sabon zabe ba. Ko da yake Firaminista Tsipras ya yi bayani dalilin da ya sa ya yi amai ya lashe kwanaki kalilan bayan kuri'ar raba gardama da aka gudanar cikin watan Yuli a kan ka'idojin bashin da ke kan kasarsa, kuma ya yi watsi da manufofinsa na yakin neman zabe. Sai dai idan aka kwatanta shi da 'yan hamayya zan a ga cewa yana gabansu, domin ya kasance cikin manyan 'yan siyasar kasar da ke da kwakkwarar shaidar cewa ba su da wata alaka da tsaffin jam'iyyun kasar da kuma shugabanninsu wadanda suka jefa Girka cikin matalolin tattalin arziki mafi muni cikin tarihinta na baya bayan nan.