Majalisar Kataloniya ta zabi 'yan aware
January 17, 2018Talla
Jam'iyyun siyasa na 'yan aware a yankin Kataloniya na Spain da suka samu nasara sun zabi Roger Torrent mai ra'ayin aware domin jagorancin majalisar dokokin yankin, abin da ake gani zai share hanyar sake zaben shugabannin 'yan aware karkashin Carles Puigdemont da suke gudun hijira domin jan ragamar mulkin wannan yanki na kasar Spain.
A wannan Laraba aka bude zaman majalisar dokokin na Kataloniya tun bayan zaben da ya wakana. Zaben ya biyo bayan matakin Firaminista Mariano Rajoy na Spain da ya rusa majalisar dokokin yankin na Kataloniya sakamakon zaben raba gardama da aka gudanar da ficewar yankin daga cikin kasar Spain a shekarar da ta gabata ta 2017.