1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar ministocin Girka ta yi murabus

November 8, 2011

Girka ta kama hanyar kafa sabuwar gwamnati bayan da ministocin ƙasar suka bayar da takardun ajiye aikin su

https://p.dw.com/p/136sa
Firaministan Papandreou ya ya da kwallo....Hoto: dapd

Majalisar ministocin ƙasar Girka ta miƙa takardar yin murabus domin bayar da damar kafa sabuwar gwamnatin ƙawance a ƙasar, a dai dai lokacin da ƙasar ke ƙara fuskantar matsin lambar neman ta kawo ƙarshen taƙaddamar siyasa daga ƙungiyar tarayyar Turai. A cewar ministan kula da harkokin yawon buɗe a ƙasar ta Girka, George Nikitiadis dake barin gado, ɗaukacin ministocin ne suka miƙawa firaministan George Papendreau, wanda shima ya bayar da sanarwar cewar zai ajiye aikin sa takardun sauka daga muƙaman nasu.

A wannan Talatar ce Papendreau ya shiga yini na biyu a tattaunawar daya ke yi tare da jagorar adawa a ƙasar Antonis Samaras game da batun kafa sabuwar gwamnati.

Ƙasar Girka dai ta faɗa cikin rigimar siyasa ne sakamakon bashin daya yi mata katutu, wanda kuma ya tilasta mata samun rancen kuɗi daga tarayyar Turai da gungun ƙasashen dake yin amfani da takardar kuɗin Euro da kuma asusun bayar da lamuni a duniya na IMF. Sai dai kuma ƙa'idojin da sassan da suka bayar da bashin suka gindaya mata, na aiwatar da shirin tsuke bakin aljihu, ya sa gwamnatin fuskantar jerin zanga-zangar yin Allah wadai da matakan, daga ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman