Majalisar Thailand ta amince da auren jinsi
June 18, 2024Talla
'Yan majalisar dokokin Thailand sun amince da dokar daidaita aure tsakanin jinsi inda ta kama hanyar zama kasa ta farko a kudancin Asia da ta amince da auren jinsi bayan kasashen Nepal da Taiwan wadanda su ma suka amince da auren jinsi.
Majalisar dattijan Thailand din ta amince da kudirin dokar wadda a yanzu za a gabatar wa Sarki Maha Vajiralongkorn domin amincewarsa.
Firaministan Thailand Srettha Thavisin, ya bayar da cikakken goyon baya ga al'ummar LGBTQ zai kuma karbi bakuncinsu a nan gaba domin shirya musu liyafa.