Majalisar Yuganda ta sauya tsarin mulki
December 21, 2017Talla
'Yan majalisar dokokin Yuganda da gagarumin rinjaye suka amince da gyara ga kundin tsarin mulki domin bayar da dama ga wadanda suka haura shekaru 75 kan tsayawa takara a zaben shugaban kasa. 'Yan majalisa 315 suka amince da shirin, yayin da 62 suka nuna rashin amincewa, kana biyu suka yi rowan kuri'a, bayan kwashe kwanaki uku muhawara.
Wannan mataki na 'yan majalisa zai share hanya ga Shugaba Yoweri Museveni dan shekaru 73 damar sake takara a zaben shekara ta 2021. Sai dai sabuwar dokar ta sake dawo da wa'adi na biyu na mulki ga shugaban kasa. Karkashin sabon matakin Shugaba Museveni da yake rike da madafun iko tun shekarar 1986 fiye da shekaru 30, zai iya ci gaba da rike madafun iko zuwa shekara ta 2031.