1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240311 UN-Menschenrechtsrat Iran

March 25, 2011

Iran ta shiga jerin ƙasashen da ke da masu bincike na musamman, ba da son ran ta ba, sakamakon rohatannin take haƙƙin ɗan Adam a ƙasar

https://p.dw.com/p/10hgq
Mahmoud AhmadinejadHoto: AP

Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da samar da mai bincike na musamman, wanda zai sa ido a alamuran da suka jiɓanci haƙƙin ɗan adam a ƙasar Iran. Hukumar ta yanke wannan shawarar ne bayan da babban sakataren Majalisar Ban Ki Moon, ya gabatar mata da wani rahoton da ke nuna cewa yanke hukuncin kisa da kuma fatattakar masu fafutukar kare haƙƙin bil adama da masu adawa da gwamnati ya zama ruwan dare a ƙasar.

A karon farko tsakanin shekaru fiye da goma, an zaɓi mai bincike na musamman wanda zai sa ido a kan alamuran kare haƙƙin bil adama a Iran a kowani lokaci. Ware mai bincike na musamman wa kowace ƙasa ba abu ne da ke da farin jini ba, ƙasashen Sudan, Somaliya, Myanmar da Koriya ta arewa ne kaɗai suke da masu bincike na musamman, kuma yanzu Iran ta shiga jerin waɗannan ƙasashen ba da son ran ta ba.

Iran Menschenrecht Aktivisten
Hoto: Maryam Mirza

A taron da aka gudanar a birnin Geneva, jakadan Iran ya yi zargin cewa sukar da ake wa alamurar da suka shafi 'yancin ɗan adam a ƙasar sa ba wani abu ba ne illa siyasa. Hadi Ghaemi lauyar kare haƙƙin bil adamar Iran  ya ƙaryata wannan zargin, kuma ya jaddada cewa gwamantin na Iran na fatattakar 'yan adawar ƙasar ne domin su tsorata duk masu adawa da gwamantai, waɗanda kuma ke da niyyar bin guguwar canjin da ke kaɗawa a yankin

"Mun yarda cewa tun a watar Janairu, gwamanatin Iran ta ke fargaba, saboda ta ga cewa abubuwan da suka faru a Iran shekaru biyun da suka gabata na yaɗuwa a yankin kuma sun ci nasara wajen kawo gagarumin sauyi. saboda haka, babban ƙalubalen da ke gaban su shine mai yiwuwa wannan guguwar zai iya kai ga kifar da gwamnatin ita kanta Iran ɗin".

Adadin waɗanda ake yanke wa hukuncin kisa a ƙasar ya ƙaru

Julie de Rivero na ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta ce rahoton ya bada bayanan cin zarafi da ƙaruwar tashe-tahsen hankula, kuma suna tunanin wannan wani mataki ne na rufe bakin masu adawa da gwamanti.

"Ina ganin mun ga ƙaruwa a danniya da take haƙƙin mutane ne tun bayan zaɓe, kuma ya cigaba da taɓarɓarewa tun lokacin, musamman  ma masu sukan gwamnati kuma hukuncin kisa shine ake amfani da shi a matakin ƙarshe."

Logo von Human Rights Watch der UNO

To amma menene mai binciken na musamman zai iya yi a ƙarƙashin ƙudurin MDD, domin dole ne Iran ta gayyace shi kafin ya iya sa ƙafa a ƙasar ta, Kuma hukumomi a Tehran basu gayyaci wani jami'in hukumar kare haƙƙin bil adama na Majalisar fa na tsawon shekaru da dama yanzu. Duk da haka dai Haidi Ghaemi ya yi ammanar cewa aikawa da mai bincike na musamman na da mahimmanci sosai.

" Bamu da wata hanya na aikawa da rahotanni ko kuma rubuta abubuwan da ke faruwa daki-daki, saboda haka muna buƙatar wani da ke da izinin MDD ya yi wannan aikin kuma ya riƙe shaidawa hukumomin ƙasa da ƙasa abubuwan da ya ke gani a zahiri. Kuma ko da ba su iya zuwa ƙasar da kan su ba, kasancewar wannan mai binciken zai iya ƙalubalantar gwamnati a fili ya kuma yi hira da waɗanda abun ya shafa zai amfani ƙasar sosai."

Abun da ya rage yanzu sai dai a sa ido gani. Hukumomi a Tehran za su gayyaci mai binciken? Idan har suka gayyace shi, za su bar shi ya yi yawo a matsayin sa na mai binciken ba tare da an takura masa ba? Idan har basu gayyace sa ba, dole ne ya rubuta rahoto bisa hujjojin da ƙungiyoyin kare bil adaman da ke ƙasar da 'yan siyasan da aka kora suka bashi. Za'a kuma gabatar da wannan rahoton a gaban wani taron da hukumar zata gudanar nan ba da daɗewa ba, daga nan sai hukumar ta san matakin da zata ɗuka.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar