1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bukaci Iran da ta yi hanzari wajen ba da amsa ga shawarwarin da aka gabatar mata.

June 28, 2006
https://p.dw.com/p/BusS

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya shawarci ministan harkokin wajen Iran, Manochehr Mottaki, da ya yi gaggawa, wajen ba da amsar ƙasarsa ga shirin nan da ƙasashen Yamma da Amirka suka gabatar mata, a yunƙurin da ake yi na shawo kan mahukuntan birnin Teheran su soke shirye-shiryensu na sarrafa makamashin nukiliya. Ƙasashen Turai da Amirkan na neman Teheran ta ba da amsa kan wannan batun ne, ba da wani jinkiri ba. Jakadan Amirka a Majalisar Ɗinkin Duniya, John Bolton, ya ce ƙasarsa na bukatar amsa ne, kafin taron da ministocin harkokin wajen ƙasashe 7 mafi arzikin masana’antu a duniya da Rasha za su yi a birnin Moscow a gobe alhamis.

A nasa ɓangaren, shugaba Mahmoud Ahmadinijad na Iran ya ce gwamnatinsa ba za ta ba da amsa ga shirin ba, sai a tsakiyar watan Agusta.