Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartad da ƙuduri kan Iran.
July 31, 2006Talla
Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya zartad da wani ƙuduri, inda ya bukaci Iran da ta dakatad da ayyukan makamashin nukiliyanta da ake ta ƙorafi a kansa, kafin ran 31 ga watan Agusta, in ko ba haka ba, ta huskanci takunkumin da za a sanya mata. Ƙudurin, mai lamba 1696, na nuna matuƙar damuwa ne ga daddagewar da Iran ɗin ke yi wa umarnin da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya Ta Ƙasa da Ƙasa ta ba ta, na ta soke duk shirye-shiryenta na inganta sinadarin yurenniyum da dai sauran wasu ayyukan sarrafa makamashin nukiliyan. Ƙasashe 14 ne suka ka da ƙuri’ar amincewa da ƙudurin, yayin da ƙasar Qatar ta kasance ita kaɗai ce mai adawa da shi.