Makamashin nukiliya a Jamus - Dangantakar soyayya da kiyayya
Da farko an yi bikin ne a Jamus, sannan aka yi Allah wadai da shi kuma a karshe an dakatar da shi. Makamashin nukiliya na kan hanyar dawowar cikin saboda rashin iskar gas daga Rasha. Waiwaye kan tarihin.
Tashar nukiliya mai alamar kwai
Tashar nukiliya ta farko a Jamus ta fara aiki a karshen watan Oktoba 1957 a Garching kusa da Munich. An sanya mata sunan ne saboda siffarta. Tashar ta zama alamar bincike na nukiliya da sabon mafari bayan yakin duniya na biyu. A shekara ta 2,000 an rufe tashar ta bincike sakamakon gaza cika ka'idojin bincike na kimiyya.
Fara amfani da Uranium don samar da makamshi
Shekaru uku bayan fara amfani da Uranium don samar da makamshi, tashar nukiliya ta farko a Kahl am Main ta samar da wutar lantarki daga 1961. Tashar wutar lantarki mafi karfi ta biyo baya, kamar hoton nan a Gundremmingen, wanda ta fara aiki a 1966.
Farkon fafutukar yaki da makamashin nukiliya
A shekarar 1973, girgizar da rikicin man fetur ya yi ya kara karfafa manufofin nukiliya. Amma zamani yana canzawa. Shakkun jama'a game da tsaftataccen makamashin da nukiliya sai ya yi ta karuwa. Adawar ta girma kuma a lokacin zanga-zangar adawa da tashar makamashin nukiliya ta Brokdorf a Schleswig-Holstein daga 1976 zuwa gaba, masu zanga-zangar da jami'an 'yan sanda sun sha yin arangama.
Alamar adawa da nukiliya
Duk masu fafutukar kare muhalli na Jamus na iya taruwa da taken "Makamashin Nukiliya? a'a mun gode" tare da murmushin rana a kan alamar rawaya. Daga tsakiyar 1970, tambarin ya kasance a ko ina a zanga-zangar adawa da makamashin nukiliya. Taken ya zama wata alama a kayan da ake fitar wa ketare a fadin duniya.
Tashin hankali bayan Harrisburg da Chernobyl
A ranar 28 ga Maris, 1979, wani mummunan hatsarin nukiliya ya faru a tashar makamashin nukiliya ta Mile Island da ke kusa da Harrisburg a Amurka. Shekaru bakwai bayan haka, a ranar 26 ga Afrilu, 1986, hatsari mafi muni a duniya ya faru a Chernobyl na Ukraine (hoto). Tashar Chernobyl ya zama alamar hadarin nukiliya.
Bullar sabuwar jam'iyya
A shekarar 1980 wata sabuwar jam'iyya ta fito a yammacin Jamus: The Greens mai rajin kare muhalli. Masu fafutukar zaman lafiya da kare muhalli da masu adawa da makamashin nukiliya ne suka kafata. Gert Bastian da Petra Kelly da Otto Schily da Marieluise Beck-Oberdorf suna murnar shiga majalisar dokokin Jamus a 1983. Yaki da makamashin nukiliya na daya daga cikin abubuwan da suka sa gaba.
Wackerdorf: Bala'i, amma kuma nasara
Za a gina cibiyar sake sarrafa matatun mai da aka kashe a wackersdorf da ke Bavaria. A lokacin wata tarzoma a cikin bazarar 1986, an kashe masu zanga-zangar da yawa da jami'i guda tare da raunata daruruwan mutane. A karshen watan Mayun 1989, an dakatar da aikin ginin. Nasarar farko ga kungiyar muhalli ta Jamus.