1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundesliga Mönchenglabdach da Bayern Munich

Mouhamadou Awal Balarabe
December 9, 2019

Wasannin karshen mako na Bundesliga da suka fi daukar hankali da irin fafatawar da aka yi tsakanin kungiyoyin kwallon kafa.

https://p.dw.com/p/3UVmq
Bundesliga Borussia Mönchengladbach gegen Bayern München
Hoto: Getty Images/AFP/U. Kraft

An shiga wasanni mako na 14 na Bundesliga, kuma wasan da ya fi daukar hankali shi ne wanda ya gudana tsakanin Borussia Mönchenglabdach da ke saman teburi da Yaya babba Bayern Munich inda aka tashi 2-1.  Ita Munich ta ga ja lokacin da dan wasanta Ivan Perisic ya zuwa kwallo minti hudu bayan dawo hutun rabin lokaci, kafin ta ga janyewa, inda Ramy Bensebaini dan wasana baya na Mönchengladbach ya farke, kuma ya zira bugun daga kai sai mai tsaron gida da suka ci gajiya.

Wannan nasarar ya bai wa Borussia Mönchengladbach damar ci gaba da cin karenta a saman teburi da maki 31. Ita kuwa RB Leipzig tana biya mata baya da maki 30 bayan da ta samu nasara a kan Hoffenheim tsohuwar kungiyar kocinsu Julian Nagelsmann da 3-1.

Ita kuwa Yaya karama Borussia Dortmund ta yi wa Fortuna Dusseldorf kaca-kaca: 5-0, ciki har da kwallaye biyu da Marco Reus da kuma Jadon Sancho suka zira kowanne su. Dan wasan tsakiya na Dortmund Julian Brandt ya bayyana nasarar da abin da kowa ya dade yana jira.