Makokin tunawa da harbo jirgin Malesiya
July 17, 2017Talla
A lokacin wannan taron makoki wanda zai gudana a wannan Litinin a karkashin jagorancin sarki William Alexander da Sarauniya Maxima na masarautar Hollande, Mutane kimanin 2000 daga cikin dangin mamatan za su yi zobe a wani shingen itatuwa 298 da aka shuka a wurin da jirgin ya fado a matsayin shaidar nuna alhini ga mutanen 298 da suka rasu a lokacin faduwar jirgin.
A ranar 17 ga watan Yulin shekara ta 2014 ne dai a tsakiyar yakin kasar Ukraine wani makami mai lizzami kirar kasar Rasha ya kakkabo jirgin na Malesiya Airlines dauke da fasinjoji 298 da suka hada da 'yan kasar Hollande 196.