Makomar Dimukuradiyya a kasashen da sojoji ke mulki
May 27, 2024Wannan na zuwa ne bayan da a kasashen Mali da Burkina Faso sojojin da ke mulkin suka tsaida wa'adin da za su yi a hakumance kafin mika mulki ga farar hula.
Tun dai bayan da hukumomin mulkin sojan kasar Mali suka sanar da tsawaita wa'adin mulkin rukon kwarya da shekaru uku, takwarorinsu na Burkina Faso wa'adin shekaru biyar a hakumance, mahawara ta kaure a tsakanin 'yan Nijar kann yadda watanni 10 bayan juyinn mulkin gwamnatin mulkin sojan Nijar ke ci gaba da yin burus da batun sanar da 'yan kasa ranar da zata soma wa'adin mulkin rikon kwarya da ba zai wuce na shekaru uku ba da shugaba Janar Tchiani ya sanar tun farko, kafin mika mulki ga farar hula. Yanzu haka Malam Ismaeil Mohamadou wani dan fafutika da kuma Malam Habila Rabiou wani matashin dan siyasa a Nijar na ganin babu bukatar gaggauta tsaida wa'adin mulkin rikon kwarya da mayar da mulki ga farar hula a Nijar ta la'akari da jerin matsalolin da suka dabaibaye kasar.
Watanni 10 bayan juyin mulkin nijar, babban taron mahawara na 'yan kasa da hukumomin mulkin sojan Nijar din suka ce shi ne zai tsayar da wa'adin mulkin rikon kwarya ya faskara shiryawa watanni 10 bayan juyin mulki. Kuma Malam Siraji Issa na kungiyar MOJEN mai adawa da mulkin soja na ganin sojojin Nijar din ba su da niyyar barin mulki, hasalima suna shiri ne na canza sheka zuwa siyasa domin ci gaba da mulkin.
To amma Malam Sahanin Mahamadou wanio matashin dan siyasa mai adawa da mulkin soja na ganin kasa tsaida wa'adin mulkin wata alama ce da ke nuni a cewa mulkin sojan na tsaka mai wuya.
Ko a ganawar da ya yi a makon da ya gabta da kungiyoyin farar hula a fadrasa, shugaba Tchiani ya sanar da su da su kara hakuri a game da batun wa'adin mulkin rikon kwarya da za su yi inda ya ce a akwai wasu batutuwa da ke a gabansu da suke son kawar da su kafin tsaida wa'adin mulkin rikon kwarya da ma alkiblar da mulkin zai dosa.