1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Makomar 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 18, 2023

A daidai lokacin da ake tunkarar zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Turkiyya, babban jagoran adawar kasar Kemal Kiliçdaroglu ya yi alkawarin korar 'yan gudun hijira daga kasar.

https://p.dw.com/p/4RXn4
Turkiyya | Takara | Zabe | Shugaban Kasa | Kemal Kilicdaroglu  | Erdogan Wahlplakat
Babban jagoran adawar Turkiyya Kemal KiliçdarogluHoto: MURAD SEZER/REUTERS

Babban jagoran adawar na Turkiyya Kemal Kiliçdaroglu ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Ankra, inda ya ce da zarar ya samu nasarar a zaben zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 28 ga wannan wata na Mayu da muke ciki. A cewarsa zai mayar da baki dayan 'yan gudun hijira kasashensu na asali, yana mai cewa zabarsa ne zai tabbatar da dorewar kasar Turkiyya. A cewarsa in har aka sake zabar shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban kasa, to tabbas za a samu karin wasu 'yan gudun hijirar miliyan 10 da za su iso Turkiyya. Ya kuma sanya kafa ya yi fatali da yiwuwar tattaunawa, ko kuma zama kan teburin sulhu da mayakan Kurdawa.