Makomar yarjejeniyar nukiliya ta Iran
May 9, 2018A wata ziyarar da ya kai birnin Washington a kwanakin baya, shugaban Faransa Emamnuel Macron, ya bayyana cewar Turai ba ta da wani shiri na daban kan yarjejeniyar nukiliyarsu da Iran. Wannan dai tamkar irin kalaman ne na siyasa, domin ba kasasfai 'yan siyasar kan fadi wani shiri na daban idan na farkon ya gaza, ko da kuwa suna da wani zabin ba. A kan haka, ka da a saran cewar 'yan siyasa da jami'an diplomasiyya za su fito fili su yi ikirarin cewar za su iya ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran ba tare da Amirka ba. Ellie Geranmayeh da ke ofishin majalisar kula da harkokin ketare na Turai na da ra'ayin cewar, kasashen da ke cikin yarjejeniyar Iran din kamar Rasha da China da Turan na iya cetonta ba tare da Amirka ba.
Ya ce: "Shekara guda ke'nan na ke nanata cewar akwai hanyar da Turai za ta iya ceto yarjejeniyar da sauran wadanda suka rattaba hannu ko Amirka ba ta ciki. Sai dai ko shakka babu aiwatar da yarjejeniyar da tabbatar da dorewarta ba tare da Amirka ba, abu ne mai kamar wuya. Wajibi ne kasashen Turai su yi tunani da nazari mai zurfi domin cimma nasarar hakan".
Yarjejeniyar mai shafuka 159, ta kunshi bayanan batutuwa dalla-dalla. A sauwake ana bukatar Iran ta takaita shirin nukiliyarta na sarrafa makamashi, tare da barin masu bincike shiga kasar, ita kuwa za'a janye wasu daga cikin takunkumin da aka kakaba ma ta a baya. Karin takunkumin dai bai shafi kamfanonin Amirka ko Iran ba, sun shafi kamfanonin wasu kasashe ne na ketare kamar Turai. Batutuwan dai sun shafi mai da iskar gas da Iran din ke fitarwa waje.