Sudan: Makomar yarjejeniyar tsagaita wuta
May 23, 2023Wannan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke kashedin rikidewar rikici tsakanin sojojin zuwa yakin basasa da na kabilanci a fadin kasar. Sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutar ta tsawon mako guda da Amurka da Saudiyya suka shiga tsakani aka cimma a birnin Jiddah, a hukumance ta fara aiki ne da misalin karfe tara da mintuna 45 na agogon Khartoum, wato karfe bakwai da mintuna 45 agogon GMT. A cewar mukaddashin ministan harkokin wajen Saudiyya, sabuwar yarjejeniyar ta sha bam-bam da wadanda aka yi ta cimma a baya. Sai dai shaidun gani da ido sun tabbatarwa kafar yada labaran al-Arabiyya cewa ba ta sauya zani ba, musamman a biranan Khartoum da Omdurman. A hannu guda kuma a wani mataki da ka iya ruru wutar rikicin, Janaral Abdel Fattah al-Burhan ya sanar da tsige madugun 'yan tawayen na RSF Janaral Mohamed Hamdan Dagalo a matsayin mataimakinsa kana ya maye gurbinsa da jagoran mayakan sa-kai na 'yan tawayen Darfur. Tuni dai mataimakin Dagalo ya siffanta matakin da na shakulatun bangaro, a wani sabon sakon murya da ya yada a shafukan sada zumunta yana mai cewa babu wana zai bi umurnin al-Burhan din.