1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makotan Libiya na adawa da shirin kasashen Yamma

Abdoulaye Mammane Amadou/ YBMarch 3, 2016

Kasashen da ke makwabtaka da Libiya na ci gaba da nuna adawarsu da kutsen sojin kasashen Yamma a kasar, yadda suka shirya gudanar da taron koli a karshen watannan a Tunusiya.

https://p.dw.com/p/1I6fI
Libyen Kämpfe in Bengasi
'Yanfafutika da makamai a birnin BengaziHoto: Getty Images/AFP/A. Doma

A taron share fage da suka gudanar a birnin Tunis na Tunusiya, ministoci da wakilan kasashen shida da ke makwabtaka da Libiya, wato kasashen Tunusiya da Aljeriya da Nijar da Chadi da Sudan da Masar sun nuna fargabarsu da kar allura ta tono garma sakamakon kutse ko hare-hare ta saman da kasashen Yamma suka fara kai wa kasar ta Libiya da zimmar murkushe kungiyar Daeish ko IS. A ta bakin ministan harkokin wajen Tunusiya, Khamis Juhainawi:

"Muna matukar fargabar cewa, kutsen ko hare-haren sojin ketare a Libiya zai iya kawo bazuwar 'yan ta'adda zuwa Tunisiya da sauran kasashen yankin don samun maboya, musamman ma a kasashen da ke da yawan duwarwatsu."

Da ma tun kafin shirya taron, shugaban kasar Tunusiya, Beji Caid Essebsi ya ce, kamata ya yi kasashen da ke shirin yakar ta'addanci a Libiya su dinga tunanin abin da zai je ya komo, musamman ma ga kasashen da ke makwabtaka da Libiyan;

Akila Saleh Issa Libyen
Akila Saleh Issa jagoran 'yan majalisa a LibyaHoto: picture-alliance/dpa/Str

"Kasashen abokanmmu da ke shirin kutse a Libiya, bai kamata ku dinga tunanin abin da zai kare muradinku ku kudai ba, idan kuka shawarcemu, mukaga matakin da za,a dauka a ya dace,zamu amince, amma kar kuyi abin da zai amfaneku kadai mu kuma ya cutar damu".

Wasu kuwa a kasar ta Tunusiya suna hangen batun kutsen ne ta bangaren zamantakewa da tattali; "Idan muka tuna shekarar 2012 ,yadda rikicin Libiya da hare haren NATO suka sanya kwararar dubun-dubatar 'yan Libiya zuwa Tunusiya, za mu kara yin adawa da wannan kutse. A yanzu haka akwai dubban 'yan Tunusiya da ke ci rani a Libiya, idan lamura suka kara dagulewa, duk nan gida za su dawo su zauna ba aikin yi."

Tunesien Libyen Anti-Dschihadisten-Zaun
Dakarun Libya da Tunusiya masu adawa da ISHoto: picture-alliance/dpa/M. Messara

Shi kuwa ministan harkokin wajen Aljeriya,Ramtane Lamamra,nuna mahimmanci karfafar sabuwar gwamnatin Libiya ya yi da ta dage damtse kasar ta zauna lafiya.