Makwabtan Libiya sun yi kira da a yi sulhu a ƙasar
August 25, 2014Talla
A cikin sanarwar bayan taron da suka yi a birnin Alƙahira na ƙasar Masar a wannan Litinin, ƙasashe masu maƙwabtaka da Libiya sun amince cewar ba za su yi katsalanda cikin harkokin ƙasar don kawo ƙarshen ruɗani da tashe-tashen hankula a ƙasar mai arzikin man fetir ba. Maimakon haka ƙasashen kira suka yi da a nemo hanyar sassanta al'ummar ƙasar. Matakin na hadin guiwar ƙasashe maƙwabtan ya dace da manufarsu ta ƙin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Libiya. Da farko jakadan Libiya a birnin Alkahira ya buƙaci gamaiyar ƙasa da ƙasa ta taimaka a samar da kariya ga rijiyoyin mai da filayen jiragen sama da kuma sauran ƙadarorin ƙasa.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane