1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali: Adawa ta gana da masu juyin mulki

Gazali Abdou Tasawa
August 20, 2020

A kasar Mali kawancen kungiyoyin M5-RFP wanda ke adawa da tsohuwar gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya bayyana gamsuwarsa da juyin mulkin da sojoji suka aiwatar a kasar.

https://p.dw.com/p/3hDlm
Mali Kati PK Putsch Anführer Ismael Wague
Hoto: Getty Images/AFP/A. Risemberg

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin juya Laraba bayan ganawa da sojojin da suka yi juyin mulkin, kawancen na M5 wanda ya hada jam'iyyun siyasa da na farar hula da ma na addinai ya bayyana cewa sojojin sun kammala aikin da dama kawacen ya fara ne na neman murabus din shugaba IBK.

 Kazalika kawancen na M5 ya ce ya amince a bisa manufa da sabuwar hukumar mulkin sojan ta Conseil National Pour le Salut du peuple ko CNSP a takaice wacce sojojin suka girka.

 Shugabannin kawancen na M5 sun kuma yi kira ga sojojin da su gaggauta girka gwamnatin rikon kwarya kuma a shirye suke su kawo tasu gudunmawa domin shata jadawalin wa'adin mulkin rikon kwaryar tare da sojojin da kuma sauran bangarorin al'ummar kasar.