1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawo karshen aikin MINUSMA a Mali

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 29, 2023

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, na shirin kada kuri'ar kawo karshen Shirin Wanzar da Zaman Lafiya na majalisar a Mali na tsawon shekaru 10.

https://p.dw.com/p/4TFNv
Mali  | Assimi Goita | Sojoji | Juyin Mulki
Jagoran juyin mulki kana shugaban gwamnatin soja ta Mali Assimi GoitaHoto: Habib Kouyate/Xinhua/IMAGO

Wannan matakin dai na zuwa ne, bayan da gwamnatin mulkin sojan Malin ta bukaci dakarun Wanzar da Zaman Lafiya na Majalisar Dinkin Duniyar da yawansu ya kai dubu 13 su fice daga kasar ba tare da bata lokaci ba. Shirin janye rundunar da ake kira da MINUSMA ya biyo bayan kwashe shekaru cikin tashin hankali da kuma yadda gwamnatin ta takaita ayyukan rundunar tun bayan da Malin ta hada gwiwa da sojojin hayar Rasha na Wagner a shekara ta 2021, abin da ya dakile ayyukan sojojin sama da na kasa na rundunar ta MINUSMA.