1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Kokarin girka rundunar kasashen G5

Salissou Boukari
July 2, 2017

Shugaban kasar Faransa Enmmanuel Macron ya sha alwashin taimaka wa rundunar kawance ta kasashe biyar na G5 Sahel da za ta yaki ayyukan ta'addanci a yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/2fmuY
Mali Truppen
Sojojin kasar Mali a birnin BamakoHoto: Reuters

Shugaban na Faransa ya ce zai zamo kakakin kasashen biyar wajen nemo kudaden gudanar da ayyukan rundunar. Sai dai kuma Macron ya ce sai sojoji da za a dauka cikin wannan runduna sun yi abun azo a gani tare da gamsar da kasashe cewa rundunar ka iya zama madogara a yakin da ake da 'yan jihadi:

Ya ce " wadannan hare-haren 'yan ta'adda na kara mana kuzarin hada karfi da karfe domin yakar ayyukan ta'addanci ga baki dayansa. A kullu yaumin muna fama da 'yan ta'adda, ko wasu malatata da ta kamata mu manta da sunayansu da ma fuskokinsu mu daukesu kawai abokan gaba da ta kamata mu ga bayansu."

Shugaba Macron ya yi wannan kalami ne a gaban Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta, da na Chadi  Idriss Deby Itno da Shugaban Mauritaniya  Mohamed Ould Abdelaziz da na Burkina Faso  Roch Marc Christian Kaboré da kuma shugaban Nijar  Mahamadou Issoufou.