Za a kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali
September 13, 2020Talla
An cimma wannan yarjejeniyar bayan tattaunawar kwanaki uku tskanin kungiyoyin fararen hula da 'yan adawa a Bamako babban birnin kasar Mali.
Kakakin shugaban juyin mulkin na Mali Mousa Kamara, ya ce sojoji za su nada kwamitin zaben shugaban gwamnatin rikon kwarya da mataimakin da za su jagoranci kasar tsawon watanni 18.
A baya sojojin da suka yi wa Ibrahim Boubakar Keita juyin mulki, sun bukaci mulkin kasar na tsawon shekaru biyu, amma matakin ya fuskanci matsin lamba daga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS da sauran kasashen duniya.