1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojoji a Mali sun yi alkawarin shirya zabe

August 19, 2020

Jagororin sojojn da suka kifar da gwamnatin farar hula a Mali sun ce za su gudanar da zabe a kasar a wani lokaci da ba su bayyana ba.

https://p.dw.com/p/3hAlZ
Unruhen in Mali | Putschistenführer Ismael Wague
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Ortm TV

Shugabannin sojojin da suka kitsa juyin mulkin kasar Mali sun ce za su mika mulki ga gwamnatin farar hula a cikin kayyadadden lokaci.  A cikin jawabinsa ta kafar talabijin mataimakin shugaban rundunar sojin sama ta Mali, Ismael Wague ya ce sun yanke shawarar karbar ragama ne domin mutane da tarihi ya shaida abubuwan da suka faru.


Sai dai a yayin da yake sanar da yin murabus daga mulki hambararren shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita a daren ranar Talata, ya ce ya sauka domin ba ya son a zubar da jini a kasar.


"Idan har wasu daga cikin sojojinmu sun yanke shawarar wai su kawo dauki, to me zan ce, ba ni da wani zabi in ba in amince da hakan ba, ba na fata a zubar da jini domin in ci gaba da mulki.''


Tun a yammacin ranar Talata kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta ce ta dakatar da Mali daga cikin kungiyar, ta kuma yi kurarin sanya takunkumi kan sojojin da suka dauki wannan matakin da ya biyo bayan watanni ana zanga-zanga da gwamnatin ta IBK kan zargin rashin shugabanci nagari wanda ya haifar da rashin tsaro da talauci ga jama'ar kasar.