Mali za ta kai wa Nijar dauki idan aka afka mata
September 24, 2023Wannan na zuwa ne bayan barazanar afka wa Nijar da kungiyar ECOWAS ke ci gaba da yi tun bayan hambarar da gwamnati Shugaba Mohamed Bazoum da sojojin suka yi.
Ko a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana a birnin New York, ministan harkokin kasashen ketare na Mali Abdouulaye Diop ya soki matakin ECOWAS na neman ta mayar da hambabaren shugaban Nijar da karfin bindiga, matakin da ya ce ka iya lalata al'amura.
A makon da ya gabata ne hukumomin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar din suka rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya kawancen tsaro da nufin yaki da kungiyoyin mayakan tarzoma ayankin Sahel.
Yarjejeniyar ta amince cewa duk wani hari da za a kai wa guda daga cikin kasashen uku, na nufin cewa an sa kafar wando guda ke nan da sauran kasashen, sannan kuma za su iya kawo wa junansu dauki cikin gaggawa tare da yin amfani da karfin soja a duk lokacin da wani mamba na kawancen ya fuskanci wata barazana.