1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta samu tallafin kayan yaki daga Rasha

Mouhamadou Awal Balarabe
January 19, 2023

Gwamnatin mulkin sojan Mali ta samu sabbin jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu daga Rasha da ke zama babbar kawarta a fannin tsaro da siyasa. Tuni ma Bamako ta ce ta fara samun nasara a yaki da ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4MSIY
Wani sojan Mali a lokacin da yake daga tutar RashaHoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/imago images

Shugaban mulkin sojan Mali Kanar Assimi Goïta da jakadan Rasha a Bamako Igor Gromyko ne suka halarci bikin karba ko mika kayayyaki da suka hada da jiragen yaki  takwas da jirage masu saukar ungulu guda biyu. Dama hukumomin kasar Mali sun saba cewa suna saye ko samun tallafi kayan yaki daga Rasha don yakar ayyukan ta'addanci, inda na karshe ya kasance a Maris da Agusta 2022.

Tun a shekaru goman da suka gabata ne Mali ke fama da yaduwar masu ikirarin jihadi da kuma mummunan rikicin na kabilanci. Amma fadar mulki ta Bamako ta yi ikirarin samun nasara a kan 'yan ta'adda a baya-bayannan, lamarin da masana suka samu sabanin fahimta a kan wannan batu.