1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi zaben raba-gardama a Mali

May 5, 2023

Gwamnatin mulkin sojan Mali karkashin Kanal Assimi Goita ta tsayar da ranar 18 ga watan Yuni mai zuwa, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben raba-gardama domin amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/4QxNS
Mali | Übergangspräsident Assimi Goïta
Hoto: Präsidentschaft der Republik Mali

Cikin wata sanarwa da gwamnatin Malin ta fitar ta ce, za a gudanar da zaben da ke zama danba na dawo da kasar mai fama da matsalar tsaro kan tafarkin dimukuradiyya a sassa dabam-dabam na Mali da kuma ofisoshin jakadancin kasar da ke kasashen waje. Yayin da yake sanar da kudirin zaben kakakin gamnatin sojan Kanal Abdoulaye Maïga ya ce za a bude yakin neman zaben a ranar biyu ga watan Yuni a kuma rufe a ranar 16 ga watan na Yuni, kamar yadda jadawalin da suka cimma da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ya tanadar.

Can baya dai gwamnatin mulkin sojan ta Mali ta sanar da nanar 19 ga watan Maris a matsayin ranar da za a gudanar da zaben raba-gardamar, kafin daga bisani a dage zuwa wani lokaci da ba a sanar ba. A watan Fabarairun shekara ta 2024 ne kuma ake sa ran sojoji za su mika mulki ga fararen hula, kamar yadda gwamnatin Kanal Assimi Goita ta alkawarta yi sakamakon matsin lamba daga kungiyar ECOWAS ko kuma CDEAO.