Abzinawa 'yan aware sun karyata gwamnatin sojan Mali
November 22, 2023Talla
Mayaka 'yan aware na Abzinawan Mali sun karyata gwamnatin sojan kasar da ta zargi samun gawarwakin dumbin mutane a kabari guda, jim kadan bayan dakarunta suka karbe iko da birnin Kidal da ke zama tungar 'yan tawayen a makon jiya.
Mayakan sun bayyana a cikin wata sanarwa da cewa shelar wani yunkurin gwamnatin Bamako ne kawai na shafa musu kashin kaji, tare da boye ainihin kisan kiyashin da suka yi a yankin a kokarinsu na rige-rigen karbe iko da yankin Kidal da ke karkashin kulawar 'yan tawaye, tun bayan soma barkewar fitina a wannan kasa.