Tunawa da Marigayi Mandela
December 6, 2023Ranar biyar ga watan Disambar 2023, rana ce da shugaban kasar Afirka ta Kudu na farko kuma jagoran yaki da wariyar launin fata Nelson Mandela ya cika shekara 10 da rasuwa. Mandela ya rasu ne ranar biyar ga watan Disambar 2013, yana da shekaru 95 a duniya. Gwagwarmayarasa kan yaki da wariyar launin fata da kuma neman 'yanci sun janyo masa girmamawa, inda har Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar haihuwarsa wato 18 ga watan Yulin ko wace shekara a matsayin ranar Nelson Mandela. Shekaru 10 bayan rasuwarsa, akwai alamar rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan Afrika ta Kudu kan abubuwan da ake tunawa da shi.
Karin Bayani: Nelson Mandela: Gwarzo ya cika shekaru 100
Shi dai Mafrigayi Nelson Mandela ya shafe shekara 27 a gidan yari domin nemawa kasarsa 'yanci, ya kuma yi yakin samar da zaman lafiya a duniya gaba daya. Mandela ya shugabanci Afrika ta Kudu na tsawon shekara 5 kacal sannan ya dankawa wani ragama bisa radin kansa. wadannan na daga cikin abubuwa kadan da suka samarwa dan gwagwammayar daraja a idon duniya.
Mandela jagoranci samar da kundin tsarin mulki da ya kawo karshen gallazawa ga bakaken fata a Afrika ta kudu. To amma shekara 10 bayan rasuwarsa, wasu 'yan kasar na ganin laifin Mandela saboda ya rika cizawa yana kuma hurawa yayin tattaunawar da ta samar da dimokradiyya da kuma 'yanci.
Ana dai gudanar da bukukuwa daban daban a fadin kasar da zummar girmama Mandela a Afrika ta Kudu, daga cikin fitattun abubuwa da ake yi akwai taron karawa juna sani na Mandela da ke gudana a ko wace shekara a birnin Johannesburg.