Mutane miliyan 6.5 sun sauke manhajar
June 18, 2020Talla
Christian Klein ya bayyana cewar, yadda mutane suka yi maraba da wannan shiri, na nuna nasarar hadakar tawagar kamfanin na SAP da na sadarwar Jamus watau Deutsche Telekom, wanda ya kai ga samar da marhajar cikin makonni shida kacal.
Jamus ta hade da sauran kasashen Turai kamar Italiya da Poland da Latvia, wajen kaddamar da manhajar, ta hanyar amfani da Bluetooth wajen gano mu'amalar mutane, tare da yin gargadi idan daga bisani an gano wani daga cikinsu na dauke da COVID 19.