Manoman Jamus sun yi zanga-zangar kare Muhalli
Dubban mutane sun yi maci a birnin Berlin tare da kira kan samar da matakai masu daurewa bisa aikin gona. Manoma sun korafin cewa ana matsa musu bisa sauye-sauyen da ake samu.
Masu kare muhalli a Jamus sun 'kosa'
Kimanin mutane 27,000 sun yi zanga-zanga a birnin Berlin na Jamus domin samar da matakan inganta aikin gona a cewa masu shirya gangamin. Gamayyan kungiyoyin da suka kosa da jan kafar da ake samu kan samar da matakan da suka dace ne suka yi wannan zanga-zangar.
Nuna masu kudi
'Yan gwagwarmaya sun fito da kudinm Euro ga mai zanga-zangar da ta yi shiga irin da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Manoma sun neman karin taimaka daga kungiyar ta EU a fannin aikin gona. A daura da wurin an yi taron ministocin aikin gona na kasashe 70 da ministar aikin gona ta Jamus Julia Klöckner ta dauki nauyi.
Karin neman kare dabbobi
Masu kare muhalli da dabbobi sun shiga zanga-zangar tare da neman sabbin manufofin gwamnati kan aiki gona su shafi jin dadin dabbobi da kare da takaita amfani da maganin kashe kwari.
Makomar manoma a gaba
Manoma sun shirya zanga-zanga da taraktocin noma fiye da 150 suka wuce ta kafar Brandenburg da ke birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Masu zanga-zangar sun zargi gwamnati kan janyo lalacewar aikin gona da fusata momanan da ke karkara. Tun shekara ta 2005 kimanin gonaki 130,000 aka rufe a Jamus.
Manoma suke dandana kudarsu
Manoma sun yi kuma zanga-zanga ta ranar Jumma'a a biranen Jamus. Sun nuna rashin yarda matakan gwamnati da 'yan gwagwarmaya suka bukata, ciki har da tantance abinci da takaita maganin kashe kwari. Manoman sun yi rubutun da ke cewa suke ciyar da 'yan gwagwarmaya. 'yan majalisa sun shiga tsaka mai wuya tsakanin manoma da 'yan gwagwarmaya da cewa matakan da ake dauka sun gaza.
Ci gaba da gwagwarmya
Ministar kare muhallin Jamus Svenja Schulze ta amince zai yi wuya "a rage farashin abinci tare da samar da matakan kare muhalli a lokaci guda." Schulze kara da cewa ana bukatar taikaon Tarayyar Turai. Kungiyar mai mazauni a binrin Brussels tana ganin zanga-zanga da dama cikin har da ta shekara ta 2009 da manoma na Faransa suka koka da faduwar farashi.