1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta rayuwa a kasashe masu tasowa

Mouhamadou Awal Balarabe SB/AMA
September 18, 2023

Yayin da kasashe marasa galihu ke ke fuskantar rikice-rikice da matsalolin sauyin yanayi irin daban-daban, wakilan duk kasashen duniya sun yi amfani da taro kan ci gaba da mai dorewa da ke gudana a birnin New-York.

https://p.dw.com/p/4WULa
Taron ci-gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya
Taron ci-gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Mike Segar/REUTERS

Manufofin 17 da kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya suka amince da su a shekarar 2015 don gina kyakkyawar makoma mai dorewa kan nan da shekarar 2030 yana da matukar muhimmanci ga fiye da rabin al'ummar duniya. Hasali ma dai, kasashe 'yan rabbana ka wadatamu na fatan dogara a kan wannan tsarin SDG wajen magance batazanar 'yunwa ko karancin abinci da ke fama da ita, tare da habaka makamashi da ake sabuntawa, baya ga samar wa msu matsakaitan shekaru aikin yi da za su iya dogaro a kai wajen samun na sa wa a bakin salati. Ko da a yayin buden taron a birnin New-York, sai da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nunar da cewar mafarkin kasashen da ke da karamin karfi ya tahallaka kan hanyoyin inganta rayuwarsu karkashin muradan ci gaba mai dorewa. Abin da António Guterres, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya nunar.

Amirka, birnin New York | Taron Majalisar Dinkin Duniya | Antonio Guterres, Sakatare Janar
Antonio Guterres Sakatare Janar na Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Mike Segar/REUTERS

Ya zuwa yanzu dai, kashi 15% na wadannan maradan ci-gaba mai dorewa ne kawai aka yi nasarar aiwatar da su, yayin da kaso mai tsoka ke tafiyar hawainiya ko ma aka kasa assasa su. Hasali ma dai, manufofin da dama na da alaka da juna kamar daga kokarin fita daga kangin talauci i zuwa samun ilimi mai nagarta da samar da ruwan sha ko makamashi mai tsafta da inganta tsarin kiwon lafiya da yaki da sauyin yanayi ko tabbatar da zaman lafiya. Sai dai rikice-rikice da matsaloli masu yawa da suka mamaye duniya a cikin 'yan shekarun sun kawo nakasu ga tsarin ci-gaba mai dorewa, kama daga annobar Covid-19 i zuwa ga matsalar sauyin yanayi da kuma uwa uba yakin Ukraine da he haddasa tsadar rayuwa a wasu sassa na duniya. Dennis Francis da ke shugabantar babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya ce ci-gaba mai dorewar bai haifar da wani ci-gaban azo a gani ba:

Amirka, birnin New York | Taron Majalisar Dinkin Duniya | Ayakha Melithafa, Matashiya daga Afirka ta Kudu
Hoto: Mike Segar/REUTERS

Shugabannin kasashe da dama da ke halartar taro kan ci-gaba mai dorewa sun kuduri aniyar aiwatar su ba tare da bata lokaci ba don tabbatar da tsarin da zai tabbatar da zaman lafiya da da kwanciyar hankalin akasarin al'ummar duniya. Sai dai kasashe masu tasowa suna fatan gani a kasa maimakon romon baka da kasashe masu arziki suka saba shafa musu. Dama dai, jami'an diflomasiyyar kasashen Yamma sun fifita batun ci gaba a wannan babban taron shekara-shekara.

Amma dai wadannan koke-koke na kasashe masu fama da talauci na iya fuskantar barazana koma baya a taron ci gaba mai dorewa, da zarar shugaban kasar Ukraine wanda ya halarci taron majalisar dinkin duniya a karon farko a ranar Talata, gabanin taron kwamitin sulhu kan rikici kasar ta Ukraine.