Manufofin gwamnatin Merkel
November 30, 2005A cikin jawabin nata shugabar gwamnatin ta Jamus tayi kira ga wakilan majalisar dokokin ta Bundestag da al’umar kasa baki daya da su ba da la’akari da kakkarfan matsayin da Jamus ke da shi du sake wani sabon yunkuri domin shawo kann matsalolinta na tattalin arziki da zamantakewar jama’a. Dangane da manufofin ketare kuwa Angela Merkel tayi nuni ne da muhimmiyar rawar da MDD ke takawa a siyasar duniya. Ta ce wani abin sha’awa shi ne ba wanda ya taba tunanin cewar za a samu wata manufa bai daya da zata hada ‚yan Christian Union da Social Democrats karkashin tuta guda, musamman ta la’akari da mummunan sabanin da aka fuskanta tsakaninsu a yakinsu na neman zabe. A yau sai ga shi sun hade karkashin wata gwamnati ta hadin guiwa a kokarinsu na shawo kann matsalolin da suka kai wa Jamus iya wuya. Su kansu al’umar kasa a nasu bangaren sun da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa wajen tinkarar wadannan matsalolin da suka hada da miliyoyin marasa aikin yi da mummunan gibi ga baitul-malin gwamnati, in ji Angela Merkel, wadda ta ci gaba da cewar:
Jamus kasa ce dake kann gaba wajen fitar da haja zuwa ketare, kuma babu wata kasa ta duniyar nan da ta cimma matsayinta wajen kirkire-kirkire. Daga baya-bayan nan ne wani babban masanin kimiyya na kasar ya samu lambar yabo ta Nobel. A baya ga haka Jamus kasa ce mai kunshe da al’adu iri dabam-dabam.
Wannan bayanin nata dai na ma’ana ne cewar kasar tana da kyakkyawar madogara domin tinkarar matsalolin dake addabarta. Muhimmin abin da take bukata a yanzun shi ne nagartattun matakai na canjin manufofinta da sabunta al’amuranta da kuma zuba jarin ‚yan kasuwa. Da zarar wadannan abubuwa guda uku sun samu to kuwa ba shakka kasar ta Jamus zata samu bunkasa. A sakamakon haka gwamnati zata samar da wata gidauniyar kyautata makoma, wacce za a tanadar mata da tsabar kudi Euro miliyan dubu 25 dangane da shekaru hudu masu zuwa. Babbar manufar gwamnatinta, kamar yadda Angela Merkel ta ninar shi ne farfado da al’amuran Jamus ta sake komawa cikin jerin kasashen Turai guda uku da suka fi samun bunkasar tattalin arziki, a cikin ‚yan shekaru kalilan masu zuwa. Domin cimma wannan burin wajibi ne a kyautata al’amuran ilimi da cude-ni-in-cude-ka tsakanin Jamusawa da takwarorinsu baki ‚yan kaka-gida. Shugabar gwamnatin kazalika ta bayyana shirin gwamnatinta na karfafa hukldodin dangantaku tsakanin kasashen kawancen arewacin tekun atlantika. Ta ce manufofi daya ne ke tsakanin Jamus da Amurka, wadanda suka hada da neman zaman lafiya da walwala da mulkin demokradiyya da kuma kamanta adalci da hakuri da juna a rayuwa ta yau da kullum. A nasu bangaren ‚yan hamayya ba su yi wata-wata ba wajen kalubalantar manufofin sabuwar gwamnatin ta hadin guiwa a fannin tattalin arziki da neman zaman lafiyar duniya. Babban abin da ya fi ci musu tuwo a kwarya kuwa shi ne karin harajin da aka yi akan kayan amfanin yau da kullum daga kashi 16 zuwa kashi 19%.