1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufofin kasashen waje na Trump kafin zabe

Abdullahi Tanko Bala AS
October 23, 2020

Tun farkon yakin neman zabensa a 2016 Trump ya fayyace karara cikin kalmomi biyu jigon manufofinsa na kasashen ketare wato ''America First'', ma'ana Amirka ce a kan gaba amma daga baya ya yi wa manufar kwaskwarima.

https://p.dw.com/p/3kMEh
USA I TV-Duell zwischen Donald Trump und Joe Biden
Hoto: Mike Segar/Reuters

Akidar yin gaba-gadi da bugun kirji da yin fito na fito sun kasance tambarin manufofin Trump kamar yadda lamarin ya jefa jami'ai cikin rudani da mamaki. Tun bayan da ya lashe zabe, Trump ya yi ta yin karan-tsaye ga kawancen hadin gwiwa na kasa da kasa. Kwanaki uku kacal da hawa karagar mulki ya cire Amirka daga kawancen kasuwanci da kasashen nahiyar Asiya da ake yiwa lakabi da Trans-Pacific Partnership. Haka kuma ya janye Amirka daga yarjeniyoyi da dama na hukumomin kasa da kasa kamar hukumar kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya da kuma yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi.

USA Donald Trump Wahlkampf in Arizona
Manufofin trum na kasashen wajen sun fi karkata ga abinda Amirka za ta fi amfanaHoto: Alex Brandon/AP Photo/picture-alliance

Bugu da kari matakin yin gaba gadi da kuma yin biris da masalaha ta kasa da kasa kamar kudirinsa na amincewa da birnin kudus a matsayin hedikwatar Israila da mayar da ofishin jakadancin Amirka zuwa can sun kasance abin tunani. Farfesa Margaret MacmMillan kwararriya a fagen tarihi a jami'ar Toronto da Oxford, kuma jami'a a cibiyar nazarin dangantakar kasashen waje ta yi tsokaci inda ta ce ''hakika Amirka ta lalata kawance mai amfani da hukumomin kasa da kasa da suka danganci haka, kuma ina gani wannan ya sa matsayin Amirka a idanun duniya ya yi rauni matuka."  

Kazalika a watan Fabrarirun wannan shekarar Trump jawo baraka bisa manufa tsakanin Amirka da kawayenta na Turai. Ya sha sukar lamirin kungiyar tsaro ta NATO da janye sojojin Amirka a Jamus da kuma kara kudin fito a kan kayayyakin Turai da ake shigar da su Amirka da kuma yin barazanar kakabawa kasar Rasha takunkumi kan shirin shimfida bututun gas na Nord Stream 2.

USA I TV-Duell zwischen Donald Trump und Joe Biden
Joe Biden da ke kalubalantar Trump na sukarsa kan irin kamun ludayin shugabancin musamman hulda da kasashen wajeHoto: Mike Segar/Reuters

A game da takaddamar cinikayya da China da cacar baki kan kamfanin Huawei, wasu da ke ganin China na cin moriyar kasuwanci fiye da fiye da kima sabanin daidaiton cinikayya tsakaninta da Amirka da kuma batun keta haddin bil Adama da ta ke yi na cewa Trump ya yi daidai a wannan bangare. A zahirin gaskiya ma dai binciken jin ra'ayin jama'a da cibiyar nazarin bincike ta Pew ta gudanar ya nuna kimar Amirka a idanun duniya ta fadi kasa wanwar, matsayin da ba a taba gani ba cikin shekaru da dama.