Manyan ƙasashe na duniya da rikicin nukiliyar Iran
October 6, 2006Ministocin harkokin waje na manyan ƙasashe shida na duniya masu ƙarfin tattalin arziki za su gudanar da taro yau a birnin London domin tattauna yadda za su shawo kan matsalar Iran da rikicin shirin ta na nukiliya. Ana sa ran Amurka tare da goyon bayan Britaniya za su nemi ɗaukar matakan ƙaƙabawa Iran ɗin takunkumi. Sai dai kuma ƙasashen Rasha da China na sukar wannan lamiri yayin da wasu ƙasashen turan kuma ke cewa akwai buƙatar tsahirtawa domin bada dama ga matakan diplomasiya. A ranar Alhamis, Iran ta sake yin kira ga yammacin turai su nemi sasanta rikicin ta shawarwari na lumana, to amma ta nanata cewa ba zata dakatar da bunƙasa makamashin Uranium ba, tana mai cewa shirin nukiliyar na samar da hasken wutar lantarki ga alumar ƙasar ta. A hannu ɗaya dai ƙasashen na yammacin turai na zargin Iran da cewa tana shirin ƙera makamin ƙare dangi ne a fakaice.