Manyan biranen Afrika na kokawa da cunkoson ababan hawa
Bunkasar da biranen Afrika ke yi ta sanya karuwar masu ababan hawan dake amfani da tituna. Masu tsara birane na kokarin rage cunkoson ababan hawa amma kuma babu kudin yin wannan aikin.
Titunan manyan biranen Afrika da cunkoson ababan hawa
Cunkoson ababan hawa da ake samu a manyan birane na kasashen Afrika da ke kudu da hamadar Sahara na karuwa cikin gaggawa. A shekaru 20 din da suka wuce motoci dubu 100 da ake samu kan titinan birnin Abijan na kasar Côte d'Ivoire sun rubanya kansu kusan sau uku. Titinan kasar ko kuma motocin haya da ake amfani da su ba za su iya jurewa wannan cunkoson ba.
Tuki tare da abokan tafiya ko fasinja
Ba kamar a nahiyar Turai ba, da wuya ka ga direba shi kadai a cikin motarsa a nahiyar Afirka. Tasi da kananan motoci kirar safa ko kiya-kiya kamar wannan da aka yi wa ado na daukar akalla mutane 20. Babura ma dai na daukar mutum biyu zuwa uku, to sai dai duk da wannan titunan nahiyar Afirka a cinkushe suke ko da yaushe.
Ba motoci ne kadai ke haifar da cinkoso ba
Hana wucewar motoci kamar yadda ya kamata a kan tituna na daga cikin abubuwan da ke haifar da cinkoso kamar yadda hukumar kiyaye haddura ta Côte d'Ivoire ta shaida. Masu sayar da abinci a kan titi irin wadannan da ake iya gani kan titunan Bouake na kasar Côte d' Ivoire na taimakawa wajen haifar da wannan matsala don su kan sanya kayansu a wajen da aka kebewa masu tafiyar kasa.
Korar masu saida kaya a kan tituna
Mahukuntan kasar Côte d'Ivoire kan yi yunkurin korar masu ciniki a kan tituna akai-akai. An rusa shaguna da dama Bouake a cikin watan Nuwaban shekara ta 2013.
Hatsari ga masu tafiyar kafa
Masu tafiyar kafa a gefen titunan kasashen Afrika kan kasance cikin hadari saboda yanayin tukin da direbobi ke yi da ma dai lafiyar motocin da suke tukawa. An hallaka kimanin mutane 600 yayin da wasu dubu 11 suka jikkata a kan titunan Côte d'Ivoire a shekara ta 2012. Galibin wadanda suka jikkatan ko suka mutu yara ne kanana.
Yawaitar Babura
Kamar yadda yake a sauran kasashen nahiyar Afrika, yanzu ana yawan amfani da babura a Bamako babban birnin kasar Mali. Ba su da tsada kuma ba su fiya fuskantar cinkosu ba kamar yadda motoci kan fuskanta. To sai dai a hannu guda su na kan gaba wajen gurbata muhalli. A kasar Benin ga misali, babura ne ke fidda sama da kashi 50 cikin dari na gurbataciyar iska a kasar.
Tsarin sufuri mai dorewa
Irin wannan tsarin sufurin yanzu haka ya yi karanci a manyan biranen Afrika. An haramta amfani da keken doki a wasu sassa na birnin Dakar din kasar Senegal bisa dalilin cikoson da suke jawowa. Amma a Rufisque da sauran yankunan na marasa galihu ana iya samun wannan nau'i na sufuri.
Rashin kudin samar da titunan karkashin kasa
A wasu nahiyoyin, manyan birane sun dau aniyar rage cinkoso a kan tituna ta hanyar zuba biliyoyi wajen samar da motocin haya na gwamnati. Birane da dama ba za su iya gina tashoshi na zamani ko tashoshin jiragen kasa irin na karkashn kasa ba. Birnin Cape Town na Afrika ta Kudu na da layuka da aka ware musamman saboda manyan motocin haya. Haka ma a birane irinsu Lagos na tarayyar Najeriya.
Jiragen kasa na cikin gari
Guda daga cikin biranen da ke da jiragen kasa shi ne birnin Dakar na kasar Senegal. Jirgin da aka yi wa lakabi da “Petit train de banlieue” wato karamin jirgin kasa na cikin gari na taimakawa mutane zuwa wasu yankunan da ke kusa da Dakar. Tallafin da gwamnati ta yi a kan wannan harka ta sanya kudin tikiti kasancewa mai rahusa sai dai layin dogon da jiragen ke amfani da su na cikin mummunan yanayi.
Muhimmanci da keke ya ke da shi
Keke dai wani nau'i ne na sufuri da ke da matukar muhimmanci a kasashen Afrika, sai dai biranen nahiyar kadan ne suka gina tituna musamman don masu amfani da kekuna. Wannan titi da ake gani a birnin Douala na jamhuriyar Kamaru yake.