1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan kasashe sun yi tir da Yuganda

May 3, 2019

Wasu jami'an diflomasiyyar kasashen Turai da Amirka sun wofinta matakin dakatar da 'yan jarida a Yuganda, wadanda ke yada shirye-shirye masu nasaba da dan adawa.

https://p.dw.com/p/3HtDz
Im Studio bei Radio Mama in Kampala.
Hoto: DW/Helle Jeppesen

Jami'an diflomasiyyar Tarayyar Turai da Amirka da ma na wasu kasashe 14, sun tir da matakin da mahukuntan kasar Yuganda suka dauka kan kafafen watsa labaran da ke tallata matashin mawakin nan da ya rikide ya zama dan siyasa wato Bobi Wine.

Hukumomi a Yugandar sun dakatar da wasu editoci na wasu gidajen radiyo da talabijin su 13 saboda yada manufofin Bobi Wine, da kuma suka labe da saba ka'idojin aiki.

Hakan a cewar jami'an diflomasiyyar, yi wa dokokin fadar albarkacin baki karan tsaye ne.

Kowace ranar uku ga watan Mayu dai na zaman ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don kare hakkin 'yan jarida a duniya.

Mr. Bobi Wine wanda ke shirin sake kalubalantar Shugaba Yoweri Musaveni na Yuganda, na da miliyoyin matasa da ke goya masa baya a kasar.