1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maroko ta lashe gasar Futsal ta Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
April 22, 2024

A karo na uku a jere, Maroko ta lashe gasar Futsal ta Afirka da aka saba gudanarwa a filin wasa da ke rufe, bayan da ta lallasa Angola da ci 5-1 a wasan karshe a ranar Lahadi.

https://p.dw.com/p/4f4MS

A karo na uku a jere, Maroko ta lashe gasar Futsal ta Afirka da aka saba gudanarwa a filin wasa da ke rufe, bayan da ta lallasa Angola da ci 5-1 a wasan karshe a ranar Lahadi. Masu masaukin baki sun samu kwarin gwiwa daga magoya baya, lamarin da ya bai wa 'yan wasan Maroko damar zuwa kwallo tun a minti na 6 da fara wasa ta kafar Soufiane Borite.

Sannan bayan 'yan mintoci kalilan, sun mayar da martani ta kafar Aderito Santo. Amma daga bisani saba kwallo da 'yan wasan Lions de l' Atlas suka yi suna juyawa ya sanya su zura kwallaye hudu a jere.

A halin da ake ciki dai, Maroko da Angola da Libya ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya ta Futsal da za a yi a Uzbekistan a karshen wannan shekara ta 2024.