Martani bisa sabon shugaban ƙasar China
March 14, 2013Ƙasashen duniya sun fara mai da martani bisa sabon shugaban ƙasar China, inda a jiya majalisar al'ummar ƙasar China ta tabbatar da naɗin Xi Jinping a matsayin shugaban ƙasa. A martaninsa shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin, bayan taya shugaban murna, ya kuma kwatanta dangantakar ƙasashen biyu a matsayin ta musamman, wanda kuma Putin yace yana fatan za a samu ƙarin hulɗa tsakanin ƙasashen biyu a mulkin sabon shugaba Jinping. Fadar gwamnatin Rasha, ta ruwaito cewa suna maraba da ziyar da sabon shugaban ƙasar ta China zai kawo a Moscow, wanda ita ce ziyar farko da sabon shugaban zai yi a wata ƙasar waje. Kazaliki a ziyar farko ta wata nahiya, ana saran shugaba Xi Jinping, zai fara kai ziyara a Afirka yayin taron ƙungiyar ƙasace masu bunƙasar tattalin arziki da aka sani Brics, wato Burazil, Rasha, Indiya, Afrika ta kudu da China. Taron dai zai gudana ne a birnin Durban na ƙasar Afirka ta kudu. ƙasashen Rasha da China dai sun hada kai, inda suka hana MDD daukar mataki kan shugaban kasar Siriya Bashar Al'Assad, bisa rikicin dake faruwa kasar ta Siriya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Saleh Umar Saleh