Martani dangane da fara tattaunawar sulhunta gabas ta tsakiya
September 3, 2010Talla
Ƙungiyar Hamas dake rike da madafan ikon zirin Gaza a yankin Paslastiwa tayi ikirarin cigaba da kai hari akan Izraela, a martanin ta dangane da tattaunawar sulhu da aka kaddamar. Kakakin ƙungiyar Hamas Abu Obeida ya shaidar da cewar Hamas ta haɗe da wasu ƙungiyoyin sa kai 13, domin tsara kaiwa Izraela hare-hare. Bayanan Jaridun ƙasashen larabawa dai na nuni da cewar, babu wani tasiri da tattaunwara zata yi, domin babu yarjejeniyar da za a iya cimma wa ba tare da ƙungiyar Hamas da Irana ba, kasar da ake zargin tana marawa ƙungiyar baya. Shugaba Mahmoud Abbas na Fatah dai shine ke wakiltar Palastinawa a wajen tattaunawar.
Mawallafiya: Zainab Mohammad Abubakar
Edita : Umaru Aliyu