Martani duniya game da matakin Iran na sarrafa Uranium
January 10, 2012Manyan ƙasashen duniya na ci gaba da bayyana takaicinsu game da sanarwa da Iran ta yi cewa ta fara sarrafa Urinium a wata tashar nukuliya ta fordo da ke da tazarar kilometa 150 da birnin Teheran. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya bayyana cewa wannan mataki zai haddasa sabuwar damɓarwa tsakanin Iran da sauran ƙasashe. Yayin da Amurika, da Ingila, da Faransa ,da Italiya suka yi kira da babbar murya ga hukumomin Teheran, da su yi wasti da wannan aniya cikin girma da arziki.
Hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nukiliya ta ƙasa da ƙasa ta zargin Iran da ƙoƙarin mallakar makamin ƙare dangi a cikin wannan tasha. Tuni dai sakatare kuɗin ƙasar Amirka ya yi tattaki i zuwa ƙasar Sin domin tattaunawa da hukumomin Beijing game da matakan ladabtarwa na bai ɗaya da ya kamata a ɗauka akan Iran.
sai dai a nasa ɓangaren wakilin Iran a hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya bayyana martanin ƙasashen duniya da neman tsokanan faɗa. yayin da shi kuma shugaban ƙasar Iran Mahmud Ahmadinedjad da ke ci gaba da ziyarar aiki a yankin latine Amirka ya ce tayar da jinjiyoyon wuya na manyan ƙasashe ba zai sa shi sauya matakin da ya ɗauka ba.
Mawallafi: Mouhamadou
Edita: Umaru aliyu