1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani ga bayyanan Tanja Mammadu

February 7, 2014

Tsohon shugaban riƙon ƙwaryar soji a Nijar Jibbo Salu da jami'yyar PNDS Tarayya mai mulki sun mayar da martani ga bayyanan da Tanja ya yi kan batun kuɗaɗen dake janyo cece-kuce a ƙasar a yanzu haka

https://p.dw.com/p/1B5DZ
Niger Tanja Mahamadou und Souley Oumarou
Tanja Mahamadou da Souley OumarouHoto: DW/M. Kanta

A jamhuriyar Nijar tsohon shugaban mulkin riƙon ƙwarya na soja
Janar Jibbo Salu ya ce a shirye yake ya bada haɗin kai ga kotu domin ta saurare shi kan batun kuɗaɗen nan miliyan 400 da tsohon shugaban ƙasar ta Niger TANJA MAMMADU ya ambata, kuma a waje guda jamiyyar PNDS TARAYYA mai mulki ta mayar da martani a kan bayannan daTanja Mammadun ya yi a kan batun waɗannan kuɗaɗen

Wani ɗan jarida ke nan a gidan talabijin na ƙasar Nijar yake karanto wanann sanarwa da ke cewa Janar Jibbo Salu ɗin ya ce yana mai farin ciki da gwamnatin ƙasar Nijar ta buɗe bincike a game da batun kuɗaɗen, anna miliyar 400 kuma a shirye yake ya bada haɗin kai ga amsa kiran kotu a duk lokacin da ta bukace shi domin bayar da bahasi a kan wanann batu na neman tantancewa yan Nijar gaskiyar lamarin.

Magoya bayan Tandja sun ce babu takardu


'Yan Nijar da dama dai ne ke zargin cewa waɗannan kuɗaɗe sun salwanta ne a lokacin juyin mulki da janar jibbo Salu ɗin ya ƙaddamar a kan Malam Tanja Mammadu a ranar 18 ga watan fabrairu na shekara ta 2010 ko kuma a lokacin gudanar da mulkin riƙon ƙwaryar da ya jagoranta. A waje guda kuma lokacin wani taron manema labarai da jamiyyar PNDS TARAYYA mai mulki ta kira a yau ta bakin sakataran yaɗa labaranta
MALAM IRO SANI ta mayar da martani tana mai cewa:

To saidai da aka tambayi Malam Iro Sani ko me zai ce da batun
ɗaruruwan milliyoyin kuɗin da Tanjan ya ce Nijar ta mallaka a
bankin raya kasashen musulmi na BID, sai ya amsa yana mai cewa:

Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaban ƙasar Nijar Mahamadou IssoufouHoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Sai dai yanzu haka duk da irin bayanan da tsohon shugaban ƙasar Malam Tanja Mammadu ya yi, ana ci gaba da samun saɓanin ra'ayi tsakanin 'yan Nijar, dangane da gamsuwa ko kuma rashin gamsuwar bayanan na sa. Sai dai ko ma me a ke ciki za a iya cewa sannu a hankali burin 'yan Nijar na sanin gaskiyar abin da ya wakana da waɗannan kuɗaɗe na ci gaba da tabbata, a daidai lokacin da sannu a hankali, mutanen da ake gani suna da ruwa da tsaki a cikin wannan lamari ke ci gaba da fitowa suna yin magana.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Pinaɗo Abdu Waba