Martani ga kalamomin shugaban Iran game da Isra'ila
August 18, 2012A jiya Juma'a ne shugaban kasar Iran Mahmud Ahamdinenijad ya furta wasu kalamai a kan kasar Isra'ila inda ya danganta kasar da mummunan ciyon kansa,abunda ya haifar da korafe-korafe daga sassa daban daban na duniya ciki har da babban saktarin Majalissar Dinkin Duniya Ban Ki-moon wanda ya nuna matukar damuwarsa ga kalaman a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin shawo kan batun makamashin kasar ta Iran da suke zargi da yunkurin kera makaman nukleya. Kalaman na Ahamadinenijad sun ne a daidai lokacin da a ke tafka mahawara a kasar ta Isra'ila a kan yuyuwar aufkawa Iran domin lalata wasu tashoshinta na nukleya. Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da shugaban ke furta kalamai masu zafi a kan Isra'ila,ko a shekara ta 2005,shugaban ya bayana a fili manufar kasarsa ta shafe Isra'ila daga doron kasa.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza