Martani ga Sakamakon Zaben Girka
June 18, 2012Gwamnatin Jamus ta bayyana jin dadinta game da sakamakon zaben majalisar dokokin Girka da ya gudana jiya Lahadi. Shugabar gwamnati, Angela Merkel ta ce kenan kasar ta Girka za ta yi abin da ke zaman wajibi akanta a matsayinta na mambar Kungiyar Tarayyar Turai(EU). Ministan kudin Jamus, Wolfgang Schaueble ya kira sakamakon zaben a matsayin kuri'ar da za ta ba da damar ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ake bukata. Kungiyar Tarayyar Turai ita kuma ta nuna gamsuwarta da sakamakon zaben. Akan haka ne shugaban hukumar zartarwar kungiyar, Jose Manuel Barroso da shugaban majalisarta, Herman von Rumpoy suka ce inda su tsawwala wa Girka matakan da ya dace ta dauka domin gyara tattalin arzkinta da sun kansu ba su ji shi da dadi ba. Ita dai Kungiyar Tarayyar Turai so take kasar ta Girka ta dawwama a matsayinta na mamba mai amfani da kudin Euro. Hakazalika kasuwannin hada hadar kudade na Asiya da Turai sun yi armashi a dangane da wannan sakamako.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala