1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani game da janyewa Iran takunkumi

Ahmed SalisuJanuary 18, 2016

Kasashen duniya na cigaba da bayyana matsayinsu ka janyewa Iran takunkumi, inda a share wasu ke tsokaci kan abin da hakan zai haifar ga kasuwar danyen mai a duniya.

https://p.dw.com/p/1HfM7
Iran Präsident Hassan Rohani Porträt
Hoto: Reuters/J. Samad

Kasar ta Iran dai ta zama abin da masu iya magana kan danganta da mai rabon ganin badi, wadda ko ana dakawa a turmi sai ta gani saboda za ta koma fagen sayar da danyen mai da iskar haskar gas da Allah ya hore mata. Dama dai kafin aza mata takunkumin karya tattalin arziki, ta na sahun gaba na kasashen duniya da suka fi arzikin man fetur da kuma iskar gas.

USA Barack Obama PK Iran Nuklear Deal
Shugaba Barack Obama ya ce matakan diflomasiyya sun taimaka wajen janyewa Iran takunkumiHoto: Reuters/Y. Gripas

Mahukuntan kasar dai da ma jama'a sun yi ta murna bayan da aka sanar da janye takunkumin. Amirka na daga cikin wanda suka yi na'am da wannan lamari har ma shugaban kasan Barack Obama ya ce wannan matai da aka kai ya nuna cewar za a iya kawar da takun saka tsakanin kasashen duniya ta hanyoyin diflomasiyya ba sai lallai an daga hakarkari ba. Shi kuwa Shugaba Hassan Rouhani na Iran cewa ya yi janye takunkumi wata rana ce da ke zaman ta tarihi ga siyasa da tattalin arzikin kasar.

Kasashen Larabawa wanda wasunsu ke zaman 'yan marina da Iran din a nasu bangaren nuna adawarsu suka yi da anye akunkumi wanda hakan ya baiwa Tehran dama ta shiga a dama da ita a harkoki da dama wanda a baya ba ta da sukunin yi. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya Abdallah Nufaisi ya ce dage takunkumin zai zama wata dama da Iran za ta iya amfani da ita wajen goyon bayan yan ta'adda da shugabannin kama karya da kara babakere da ta ke yi a yankin gabas ta tsakiya.

Saudi Arabien König Salman
Saudiyya ta ce janyewa Iran takunkumi zai bata kwarin gwiwar cigaba da dagula lamura a yankin gabas ta tsakiya.Hoto: picture-alliance/AP Photo/K. Mohammed

Su kuwa masana tattalin arziki a nasu bangaren na cewar dawowar da Iran ta yi cikin fagen kasashen da harkoki na man fetur wani yanayi ne da zai iya taimakawa wajen sake rusa farashin danyen din duba da irin yawan man da ta ke hakowa a kowacce rana da ma irin fafutukar da za ta mamaye kasuwannin da wasu kasashen ke da ita musamman a kasa kamar Indiya wanda ke cikin jern kasashen da ke kan gaba wajen sayen danyen mai a duniya.