Ci gaba da binciken gwamnan Kano duk da umurnin kotu
November 7, 2018Masana da sauran Jama'a na ci gaba da martanin kan matakin da majalissar dokokin jahar Kano da ke Najeriya ta dauka na ci gaba da bincikien Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar bisa zargin sa da karbar na goro a hannun 'yan kwangila, wanda jaridar Daily Najeria ta wallafa hoton bidiyon da ke nuna gwaman na karbar na goro a hannun 'yan kwangila, duk kuwa da cewar wata babbar kotu a jihar ta ba da umarni ga kwamitin da ke gudanar da binken kan dakatar da ci gaba da binciken.
Kwammitin nan majalisar dokokin jihar ta Kano ya ce za su ci gaba da bincken da suka fara game da neman sanin gaskiyar, saboda umurnin da kotu ta bayar bai hana su gidanar da aiki ba. Sai dai lamarin ya janyo martani inda wasu lauyoyi ke ganin ya dace majalisar dokoki ta bi umurnin kotu, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci, kamar yadda kotun ta bukata.